FA ta musanta cin zarafin su Ferdinand

england san marino
Image caption Ingila ta ci San Marino 8-0

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta ce za ta rubuta wa Fifa cewa ba ta sami wata shedar zargin cin mutuncin Rio da Anton Ferdinand da aka yi ba.

Ana zargin magoya bayan Ingila da rera wakokin nuna wariyar launin fata a kan 'yan wasan da 'yan uwane guda biyu a lokacin wasan Ingila da San Marino na neman zuwa gasar Kofin Duniya.

Kungiyar yaki da wariyar launin fata a kwallon fata a kasashen Turai, Fare ita ce ta gabatar da korafin ga Fifa.

Ko da ike hukumar FA din ta Ingila ba ta musanta rahotannin aukuwar lamarin ba amma kuma ta ce ba ta sami wata sheda a kai ba.

Kociyan Ingila Roy Hodgson bayan wasan da Ingila ta ci 8-0 ya ce shi kam ya ji wakokin cin mutuncin.

Ya ce ''ni ba kurma ba ne, amma kuma ba bu abin da zan ce a kai.''

An gayyaci Rio Ferdinand wasan Ingila da Montenegro na neman zuwa gasar Kofin Duniya a karon farko tun 201.

Amma dan wasan na Ingila ya ki amsa gayyatar saboda ya ce zai je a duba lafiyarsa a lokacin.

Sai kuma ya tafi Qatar ya yi aiki a matsayin mai fashin baki a shirin talabijin a kan wasan na Ingila da San Marino.

Fifa za ta yanke hukunci a kan lamarin idan ta karbi wasikar da FA ta Ingila za ta gabatar mata ranar Talata da kuma duk wata sheda da take da ita.

Idan zargin ya tabbata hukumar ta FA ka iya fuskantar tara ko kuma a sa Ingila ta yi wani wasanta ba tare da 'yan kallo ba.