Davis : Birtaniya ka iya haduwa da Spaniya

andy murray
Image caption Andy Murray na daga 'yan wasan Birtaniya na gasar Davis

Da alamu 'yan wasan Birtaniya za su hadu da na Spaniya ko Switzwerland a gasar kofin Davis ta 2013.

'Yan Spaniyan dai sun hada da Rafeal Nadal su kuma na Switzerland suna da Roger Federer.

Kungiyar 'yan wasan Birtaniyan ta hada da Andy Murray.

Birtaniya ta samu kanta a hakan ne bayan da ta yi nasara a kan Rasha da maki3-2 a wasansu ranar Lahadi.

A ranar Labara ce za a shirya yadda kasashen za su kara a wasannin da za a yi ranar 13 zuwa 15 ga watan Satumba.

Bayan Spaniya da Switzerlan sauran kasashen da ake ganin zasu iya haduwa da Birtaniyan su ne Austria da Crotia da Jamus da Australia da Belgium da kuma Japan.

Inda Birtaniyan za ta yi wasan ya dogara ne da yadda a ka shirya haduwar kasashen da kuma wurin da suka fafata a haduwarsu ta baya.

Kungiyar 'yan wasan Birtaniyan ta hada da Andy Murray.