City za ta dauki kofi a badi - Mancini

Manajan kulob din Manchester City, Roberto Mancini
Image caption Roberto Mancini ya ce Man City za ta yi shirin daukar Premier badi

Kociyan Manchester City Roberto Mancini ya ce kulob din zai iya daukar kofin gasar premier a kakar wasanni mai zuwa, bayan cire rai a bana.

City dai na biye da Manchester United dake kan gaba a gasar, inda kulob din ya rage tazarar makin dake tsakaninsu zuwa 12, bayan doke abokan hamayyar tasa a Old Trafford.

"Mun san cewa a badi za mu iya daukar kofin, amma a bana kam mun yi kura-kurai." Inji Mancini.

Ya kara da cewa "Abin dai babu dadi, amma ba yadda muka iya domin a bana kam mun rasa kofin."

Kwallon da Sergio Aguero ya zura a sulusin karshe na wasan, bayan da ya canji Samir Nasri ita ta baiwa City nasara a kan United a karo na biyu a jere.

"Kakar wasannin ta kawo karshe" a cewar Mancini.

Karin bayani