Neville zai bar Everton

phil neville
Image caption Phil Neville bayan kwallon kafa gwanin kurket ne

Dan wasan baya na Everton Phil Neville zai bar kungiyar a karshen kakar wasanni ta bana

Tsohon dan wasan na Ingila wanda ya koma kungiyar daga Manchester United a watan Agusta na 2005 zai kare kwantiraginsa da klub din a watan Yuni mai zuwa.

Sai dai ya ce ba zai sabunta kwantiraginsa da kungiyar ba kuma ba wai zai bar wasan ba ne.

Ya ce ''ina son cigaba da wasa a matakin Premier iya lokacin da zan iya, amma zan yi shawara kafin sanin inda zan nufa.''

Dan wasan mai shekaru 36 sau 25 yana buga wa Everton wasa a bana kuma gaba daya sau 303 yana mata wasa.

Neville wanada bayan kwallon kafa gwani wasan kurket ne kawo yanzu ya buga manyan wasanni sama da 500.

A lokacin bazara Neville zai taya kociyan kungiyar Ingila ta 'yan kasa da shekara 21 Stuart Pearce aiki a lokacin gasar kofin Kasashen Turai a Isreala.

Karin bayani