Barcelona ta kai wasan kusa da karshe

barcelona da paris saint germain
Image caption Barcelona ta ci kwallonta ne bayan Messi ya shigo

Kungiyar Barcelona ta sami zuwa wasan kusa da na karshe na Kofin Zakarun Turai.

Zakarun gasar sau hudu Barcelona sun sami damar ce bayan sun tashi 1-1 a karawarsu ta biyu a Camp Nou da Paris Saint Germain.

Dan wasan PSG Javier Pastore ne ya fara cin Barcelona a minti na 50, kafin Pedro ya rama wa Barca a minti na 70.

Shigowar Messi wanda ya ke fama da rauni a cinyarsa ta baiwa Barcelonan karfin guiwar rama kwallon.

A wasan farko a Paris sun tashi 2-2, a wasannin biyu 3-3 ke nan sakamakon.

Barcelona ta samu galaba saboda kwallaye biyu ta jefa a ragar PSG a Paris.

A ranar Juma'a za a fasalta yadda kungiyoyin da suka shiga wasan kuda da karshen zasu hadu.