Fifa za ta hukunta Equitorial Guinea

blatter da hayatou
Image caption Fifa ta hukunta wasu kasashen Afrika saboda rashin cancantar 'yan wasansu

Equitorial Guinea na fuskantar hadarin karbe mata nasarar da ta samu a kan Cape Verde ta wasan zuwa gasar Kofin Duniya saboda sanya dan wasan da bai cancanci zama dan kasar ba.

Hukumar kwallon kafa ta duniya tana gudanar da bincike domin ladabtar da Equitorial Guinean bayan galabar da ta samu 4-3 a Malabo a wasan ranar 24 ga watan Maris.

Babu ko da daya daga cikin dukkanin 'yan wasan da suka bugawa Equitorial Guinea wasa a ranar da aka haifa a kasar.

Sai dai Fifa ta bada dama ga dan wasan da aka haifi wani daga cikin iyayensa ko kakanninsa a kasa ya bugawa kasar wasa.

Hukumar ta Fifa ba ta bayyana sunan dan wasan da ake binciken rashin cancantar tasa ba.

Kasashen Burkina Faso da Gabon da Sudan dukkanninsu an rage musu maki a wasanninsu na neman zuwa gasar kofin duniya saboda amfani da 'yan wasan da basu cancanta ba.