Lambert - Benteke ya fi fam miliyan 25

christian benteke
Image caption Benteke ba na sayar wa ba ne in ji Lambert

Kociyan Aston Villa Paul Lambert ya ce dan wasan kungiyar na gaba Christian Benteke ya kai darajar sama da fam miliyan 25.

Amma kuma ya ce ba shi da niyyar sayar da danwasan mai shekaru 22 dan kasar Belgium wanda ya syo a kan fam miliyan 7 daga kungiyar Genk a watan Agusta.

Lambert ya ce dan wasan ba na sayarwa ba ne amma duk wanda ke bukatar sa sai ya shirya kashe kudi.

Kociyan ya kara da cewa '' ba zamu hana mutnae kallonsa ba amma yanzu yana karkashin kwantiraginmu.

Kuma yana jin dadin wasansa a yanzu sannan kuma yana tashe''

Benteke ya ci wa Aston Villa kwallaye 15 a wasannin Premier na bana.

Kungiyar Tottenham ta na nuna sha'awarta a kan wasan, wanda kociyan bai nuna alamun kara armashin kwantiraginsa ba a yanzu.

Shi ma kociyan Blackpool Paul Ince a makon da ya wuce ne ya ce dansa Thomas mai shekara 21 shi ma ya kai fam miliyan 25.

Dan wasan wanda yake buga wa kungiyar baban nasa Liverpool da Reading na harin sayen sa a watan Janairu.