Za a fara amfani da na'ura a Premier

fasahar tantance shigar kwallo raga
Image caption Alkalan wasa kan hana kwallon da ta tsallaka layi

Kungiyoyin kwallon kafa na Premier ta Ingila sun amince da fara amfani da na'urar fasahar tantance shigar kwallo raga daga kakar wasanni ta gaba.

Daga na'uo'in na'urar fasahar dabam daban kungiyoyin na Ingila sun zabi wadda wani kamfanin Birtaniya ya ke yi mai suna Hawkeye (wato idon mikiya) wadda daman tuni ake amfani da ita a wasannin tennis da kurket.

Kamfanin ya ce na'urorinsa da ke daukar hoto cikin hanzari kamar walkiya za su iya tantance wurin da kwallo ta sauka kuma su sanar da alkalin wasa cikin 'yan dakikoki.

A wasannin kwallon kafa dabam daban a kwai lokutan da kwallon ta shiga raga amma alkalan wasu su ki amince wa.