Arsenal ta doke Norwich da ci 3

arsenal
Image caption 'Yan wasan kungiyar kwallon kafa na Arsenal

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta zira kwallaye uku a mintuna bakwai na karshe inda ta doke kungiyar kwallon kafa ta Norwich abun da kuma ya sa yanzu ita ce ta uku a gasar Primiya .

Da farko kungiyar Norwich ce ta fara zira kwallo a cikin ragar Arsenal a lokacinda Michael Turner ya jefa kwallon da ka.

Sai dai dan wasan Arsenal Mikel Arteta ya maida martani bayan da Arsenal ta samu damar buga fanaliti sakamakon irin wasan da Kei Kamara ya yi wa Olivier Giroud.

Fanalitin da aka ba Norwich ya karya lagwon yan wasan kwallon kafa na kungiyar kuma da ya kasance nasara ta uku da kungiyar za ta yi tun bayan na ranar 15 ga watan disemba sai dai hakan be yu ba.