Chris Hoy gwanin wasan keke na shirin ritaya

Image caption Chris Hoy ka iya yin ritaya nan gaba kadan

Sir Chris Hoy wanda ya rike kambun gasar tseren keke sau shida ana tsammanin zai bada sanarwar ritayar sa ranar Alhamis.

Gwanin mai shekaru 37 dan kasar Scotland zai yi taron manema labarai a gidansa dake birnin Edinburgh inda ake tsammanin zai bayyana matsayin nasa ga jama'a.

Hoy ya samu nasanar samun lambar yabo ta zinariya a gasar wasannin tsalle-tsalle da aka yi a birnin London na shekara ta 2012.

Amma ba a sani ba ko Hoy, zai yi ritayar nan take ko kuma zai ci gaba har sai ya yi gasar wasannin kasashen kwaman walth wanda za a yi a Glasgow a shekara ta 2014.

Karin bayani