Cardiff City ta cancanci Premier - Mackay

'yan wasan cardiff city
Image caption A karon farko tun 1962 Cardiff City za ta shiga Premier

Kociyan Cardiff City Malky Mackay ya ce kungiyar ta cancanci shiga gasar Premier.

Kuma a yanzu ta manta da dukkanin matsalolin da ta yi fama da su.

Maki daya kacal ya rage mata ta cancanci shiga Premier yayin da za ta kara da Charlton Athletic a gida a ranar Talatar nan.

Wannan shi ne karon farko a tarihin kungiyar na sama da shekaru hamsin da za ta shiga gasar Premier.

Gasar lig din kwallon kafa mafi kudi da kuma girma a duniya.

Kungiyar ta Cardiff City ta yi fama da matsaloli dabam-daban na kudi da sauransu har ta kai a 2001 ta fadi zuwa tsohon rukuni na uku na Ingila.