Oscar Pistorius ba zai shiga wasannin Landan ba

oscar pistorius
Image caption Pistorius ba zai shiga gasar wasannin Landan ba don kada hankula su karkata a kansa

Zakaran tseren nakasassu na Olympics Oscar Pistorious ba zai shiga gasar wasannin bazara ta Landan ba.

Pistorious mai shekaru 26 wanda ya ke zaman beli bayan da aka tuhume shi da laifin kisan buduwarsa Reeva Steenkamp ya na da damar shiga gasar kafin zaman shari'arsa.

Gasar ta hada da wasannin nakasassu na rana daya.

Sai dai kuma shugaban hukumar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta Birtaniya Ed Warner ya ce Pistorious ba zai shiga gasar ba.

Shugaban ya ce ''ba wai magana ce ta Pistorious ya na da laifi ko ba shi da laifi ba batu ne na yadda za ka tafiyar da harka da mutumin da ya ke da wannan zargi a kansa.''

Ya ce baya son ganin gasar ta zama wani abu da 'yan jarida za su karkatar da hankulansu daga gareta zuwa kan Mr Pistorious.

Mr Ed ya ce muddin dan tseren ya shiga gasar to ba shakka hankula za su karkata gareshi kacokan.