Karin kudi ga wadanda su ka fadi daga Premier

kungiyar reading
Image caption Reading da QPR da kuma Wigan ne ke cikin hadarin faduwa daga Premier

Daga kakar wasanni ta badi kungiyoyin da suka fado kasa daga gasar Premier za su sami karin kudin tallafi har fam miliyan 60.

Kungiyoyin a yanzu su na samun fam miliyan 48 ne na tallafin daga hukumar gasar Premier a tsawon shekaru hudu.

Sai dai kuma har yanzu hukumar ta Premier ba ta gai ga matsaya a kan yawan kudin da za ta rinka baiwa kungiyoyin ba.

Yayin da ake neman kammala maganar bada kudaden tallafin.

Tun daga shekarar 2010 kungiyoyin da su ka fado daga Premier su ke samun fam miliyan 16 a kowace kakar wasa har shekaru biyu.

Sannan kuma a ba su fam miliyan takwas-takwas a kakar wasannin biyu na gaba.

Jumulla kowace kungiya ta na karbar fam miliyan 48.

Yanzu dai kungiyoyin Readind da QPR da Wigan ne ke kan gabar fadowa daga gasar ta Premier.