Nadal na bajinta a Monte Carlo

rafeal nadal
Image caption Rafeal Nadal na harin kofi na tara na Monte Carlo

Rafeal Nadal mai rike da kofin gasar tennis ta kwararru ta Monte Carlo ya ci gaba da samun nasarar da ya ke yi a gasar.

A wannan karon ya yi galaba ne a kan Marinko Matosevic dan Australia da ci 6-1 6-2.

Da wannan nasara Nadal ya shiga zagaye na uku na gasar ta kwararru ta Monte Carlo.

Zakaran dan kasar Spaniya mai shekaru 26 ya na kokarin daukar kofin gasar ne na tara inda a yanzu ya yi wasanni 43 ba tare da an yi nasara a kansa ba.

A karawarsa da Mikhail Youzhny Novak Djokovic daya daga cikin zakarun wasan na tennis ya yi galaba a kan abokin karawar tasa da maki 4-6 6-1 6-4.

Djokovic ya farfado ne daga baya bayan Youzhny dan Rasha wanda shi ne na 27 a jerin gwanayen tennis na duniya ya shiga gabansa da maki 4-0 a turmin farko.

A ranar Talata Djokovic mai shekaru 25 ya sanar cewa zai shiga gasar bayan jiyyar raunin da ya yi a idan sawu.