Libya za ta gina filayen wasa 11 don gasar Afrika

filin wasa a libya
Image caption Libya za ta gina filin wasa mai mazaunin mutane 60,000 don gasar Kofin Afrika ta 2017

Libya za ta kashe sama da dala miliyan 300 wajen gina filayen wasa domin gasar Kofin Kasashen Afrika na kwallon kafa ta 2017.

Mataimakin frai ministan kasar Awad Ibrahim Elbarasi ya ce sun kuduri hakan ne da fatan wasan kwallon kafa zai taimaka wajen sake hada kan al'ummar kasar bayan juyin juya halin da ya kawar da Muammar Gaddafi.

A halin da ake ciki kuma Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta dage haramcin da ta dora wa Libyan na gudanar da wasanni a cikin kasar.

Kungiyoyin kwallon kafa na Libyan dai kafin dagewar su na wasanninsu ne a wasu filayen yayin da kungiyar kasar kuma ta ke wasanninta na gida a Mali da Masar da Tunisia a watanni 24 da suka gabata.

A da dai Libya ce aka tsara za ta karbi bakuncin gasar kwallon kafa ta kasashen Afrika ta 2013.

Amma sakamakon halin da kasar ta shiga na yaki da rashin tsaro aka baiwa Afrika ta Kudu wadda da ita aka tsara za ta gudanar da gasar ta 2017.