Wigan za ta tsira a Premier - Martinez

kocin wigan roberto martinez
Image caption Martinez na ganin Wigan na farfadowa a yanzu

Kociyan Wigan Roberto Martinez na da kwarin guiwa Wigan za ta tsira daga faduwa daga Premier.

Kociyan ya na ganin idan 'yan wasansa su ka dage da wasa kamar yadda su ka yi da Manchester City a wasanninsu 6 na karshe za su tsira.

Carlos Tevez ne ya ci Wigan din kwallo daya a kusa da karshen wasan sai dai kungiyar ta kai wa City hare-hare da dama.

Wasan shi ne na biyu da Wigan ta yi rashin nasara a wasanni tara.

Wigan ita ce ta 18 a jerin kungiyoyi 20 a Premier da maki 31 a wasanni 32.

Tana cikin wadanda suke cikin hadarin faduwa daga gasar.

A kakar wasanni biyu da su ka gabata sai a kusan wasannin karshe Wigan ta tsira daga faduwa daga Premier.