Chelsea na zawarcin Andre Schurrle

Chelsea
Image caption Rigar kungiyar kwallon kafa ta Chlesea

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta tattauna da kungiyar kwallon kafa ta Bayern Leverkusen game da dan wasan gaba na kasar Jamus dake son ya sauya sheka zuwa Chelsea.

Dan wasan mai shekaru 22 ya zira kwallaye 11 ga kungiyar Leverkusen ta Bundesliga a kakar bana.

'Rudi Voller da Micheal Reschke daga kungiyar Leverkusen sun yi tattaunawa da wakilan Chelsea a jiya". A cewar wani jami'in hulda da jama'a na kulob din.

" Ba a cimma matsaya ba tukunna. Kuma ba za mu yi karin haske ba a yanzu".

A shekarar 2011 ne Schurrle ya soma taka leda a kungiyar Leverkusen daga kungiyar kwallon kafa ta Mainz bayan da suka cimma matsaya kan yarjejeniyar buga wasa na tsawon shekara biyar.

Idan Schurrle ya koma Chelsea, zai kasance dan kasar Jamus na biyu a kulob din a yanzu, inda zai hade da Marko Marin, wanda ya koma Chelsea daga kulob din Werder Bremen.