Carrick da Bale da Suarez na takarar samun lambar yabo

Luis Suarez
Image caption Luis Suarez

Dan wasan kwallon kafa na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Micheal Carrick na cikin jerin sunaye shida da kungiyar kwararrun 'yan kwallon kafa ta zaba domin bawa lambar yabo ta gwarzon dan kwallon kafa ta bana.

Gareth Bale, da Robin Van persie, da Luis Suarez da Eden Hazard da kuma Juan Mata na cikin wadanda aka zaba a matsayin sun cancanci lambar yabon.

Bale da Hazard na kuma cikin wadanda ke takarar samun lambar yabo ta gwarzon matashin dan kwallon kafa, tare da Christian Benteke, Romelu Lukaku, da Danny Welbeck da kuma Jack Wilshere.

Bale shi ne aka baiwa lambar yabo ta kungiyar kwararrun 'yan kwallon kafa a shekarar 2011 a lokacin yana da shekaru 21 yayinda Van Persie shi ne zakara a bara.

A bana gasar ke cika shekara 40 da kafuwa da Norman Hunter dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Leeds United ya kasance dan wasan farko da ya taba lashe kambun.

A ranar 28 ga watan Aprilu za'a bayyana zakaran bana.