Rodgers zai yi nazari kan cizon da Suarez ya yi

Image caption An zargi Luis Suarez da cizar Branislav Ivanovic

Mai bada horo na Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Brendan Rodgers ya ce zai sake kallon hoton video na talabijin kan cece kucen da ake yi cewa Luis Suarez ya ciji Branislav Ivanovic na Chelsea.

Dan gaban Reds, ya yi arangama ne da dan bayan dan kasar Serbia a zagaye na biyu na wasan da aka tashi da ci biyu da biyu.

Mai bada horon na Liverpool Brendan Rodgers ya shaidawa BBC cewa ba zai ce ko mai ba har sai ya yi nazarin videon.

Mai bada horo na rikon kwarya na Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Rafael Benitez shi ma yaki yace uffan kan batun cizon.

Suarez din dai an taba hana shi wasanni bakwai saboda cizon dan wasan Kungiyar kwallon kafa na PSV, Otman Bakkal a watan Nuwamba na 2010.

Karin bayani