Kociyan Kamaru ya ce ya kadu

jean-paul akono
Image caption Jean-Paul Akono na rikon kwarya tun shekarar da ta wuce

Kociyan Kamaru Jean Paul Akono ya ce sanarwar da ma'aikatar wasannin kasar ta bayar cewa tana neman sabon mai horadda 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasar ta kada shi.

Kociyan na kungiyar Indomitable Lions yana rike da mukamin ne tun watan Satumba ba tare da kwantiragi ba.

Akono ya ce labarin da ya ji ta gidan Rediyon kasar ya bashi kunya tare da kada shi saboda tuni ana tattanawa game da batun bashi kwantiragin aikin.

A shekarar da ta wuce ne aka nada Akono a matsayin kociyan rikon kwarya domin maye gurbin Denis Lavagne dan Faransa.

A sanarwar neman kociyan da ma'aikatar wasanni da hukumar kwallon kafa ta kasar suka bayar sun ce duk mai sha'awar neman mukamin yana da wa'adin zuwa ranar Alhamis ya mika takardarsa.

Shirin sauya mai horadda 'yan wasan ya zo ne makwanni 4 bayan Kamarun ta ci Togo 2-1 a wasan neman zuwa gasar Kofin Duniya inda Akono ke rike da mukamin, kuma watanni biyu kafin sauran wasannin kasar biyu na rukuni