An dakatar da Suarez daga buga kwallo

Luis Suarez

An dakatar da dan wasan Liverpool, Luis Suarez, daga buga wasa har goma anan gaba, a sakamakon cizon da yayiwa dan wasan Chelsea, Branislav Ivanovic, a karshen mako.

Hukumar kula da wasannin kwallon kafa ta Ingila ce ta yiwa Suarez wannan hukunci. Hakan ya biyo bayan wata hukuma mai zaman kanta da ta gana a London domin tantance matsayin Suarez

Suarez ya amsa cewar ya aikata ba daidai ba a wasan da aka tashi 2-2 tsakanin Liverpool da Chelsea da aka buga ranar lahadi.

Dama dai a watan Disamba na shekara ta 2011 an taba dakatar da Suarez buga wasa takwas saboda yin kalamai na nuna banbancin launin fata akan dan wasan Manchester United, Patrice Evra.