Europa : Chelsea ta yi rawar gani

FC Basel da Chelsea
Image caption Chelsea na kan hanyar kafa tarihin daukar kofin Europa bayan ta dauki na Zakarun Turai a jere

Chelsea ta bi FC Basel ta Switzerland har gida ta yi galaba a kanta da ci 2-1 a wasan kusa da na karshe na kofin Europa.

Minti 12 da fara wasan wata kwallo da Frank Lampard ya bugo a bugun gefe ta taba Victor Moses a fuska ta fada ragar 'yan Basel.

Wannan ita ce kwallo ta uku da Moses ya ci a gasar ta Europa.

Masu masaukin bakin sun rama kwallon ana sauran minti 3 lokacin wasan ya cika da bugun fanareti da Fabian Schar ya ci.

Alkalin wasa ya bada bugun daga kai sai mai tsaron gidan ne bayan da Cesar Azpilicueta na Chelsea ya kayar da Valentin Stocker.

Sai dai kuma Chelsea ta sami bugun tazara a minti na 94 na wasan inda David Luiz ya fakaici 'yan FC Basel ya kwarara musu kwallo ta biyu a raga.

Kuma wannan bugun shi ne na karshe a wasan.

Ashley Cole wanda ya dawo wasa bayan jiyyar rauni da ya ji a cinya tun 1 ga watan Afrilu ba zai buga karawa ta biyu ba saboda katin gargadi da alkalin wasa ya bashi saboda bata lokaci.

Fenerbahce da Benfica

A daya wasan da aka yi tsakanin Fenerbahce da Benfica shi ma na kusa da karshe na kofin na Europa, Fenerbahce ta yi nasara da ci 1-0.

Egeman Korkmaz ne ya ci wa masu masaukin bakin 'yan Turkiyya kwallon da ka a minti na 72.

Benfica ita ce kadai kungiyar da ta taba zuwa wasan kusa da na karshe a cikin kungiyoyi hudu na yanzu da ke wasan na Europa.

Tun da Barcelona da Celtic suka fitar da Benfica daga gasar Zakarun Turai a matakin wasan rukuni in banda yanzu ba a yi galaba a kansu ba a gasar ta Europa.

Ita kuwa Fenerbahce tana kokarin zama kungiyar Turkiyya ta farko da za taje wasan karshe na kungiyoyin Turai tun bayan da Galatasaray ta dauki kofin Euefa a karawarta da Arsenal a 2000.