Kociyan Fenerbahce na cike da doki

Aykut Kocaman
Image caption Aykut Kocaman ya ce Fenerbahce ta sami gagarumar nasara

Kociyan Fenerbahce Aykut Kocaman ya bayyana haduwar da kungiyarsa za ta yi ta farko da Benfica a wasan kusa da karshe na kofin Europa da cewa ita ce mafi muhimmanci a tarihinsu.

Kungiyar tasa ta kasar Turkiyya ta sami zuwa wasan kusa da karshen ne na gasar Turai a karon farko bayan da ta buge Lazio a wasan gab da na kusa da karshe.

Kociyan ya ce ''wannan gagarumin cigaba ne.

Zamu yi kokarin ganin hakan ya dore a shekaru masu zuwa.''

ya ce ''wannan shi ne karon farko da muka sami zuwa wasan kusa da karshe a tarihinmu , Benfica kuwa sun jima suna zuwa.''

Benfican wadda ta sami zuwa wasan kusa da karshen bayan da ta yi nasara akan Newcastle da ci 4-2 jumulla gida da waje, za ta yi wasan ne ba tare da kyaftin din ta ba Luisao.

Dan wasan dan Brazil ya ji ciwo ne a cinyarsa, haka suma 'yan wasanta na tsakiya Enzo Perez da Andre Almeida sun yi rauni.