Rodgers ya soki FA kan hukuncin Suarez

Luis Suarez da Branislav Ivanovic
Image caption Suarez ya amsa laifin cizon Ivanovic

Kociyan Liverpool Brendan Rodgers ya soki Hukumar kwallon kafa ta Ingila FA a kan hukuncin da ta yanke wa dan wasansa Luis Suarez.

Hukumar ta yi wa Suarez hukuncin hana shi buga wasanni goma saboda cizon dan wasan Chelsea Branislav Ivanovic a lokacin karawarsu ranar Lahadi da suka tashi 2-2.

Kociyan ya ce hukumar ta hukunta dan wasan ne maimakon yi masa hukunci daidai da laifin da ya aikata.

Rodgers ya kara da cewa ''wannan hukunci ne kawai ba da nufin taimaka masa ya gyara halinsa ba.''

Ya ce ''idan da haramcin buga wasanni shida ne kawai da kuma dakatar da shi a wasu shida da watakila ba bu wanda zai yi korafi.''

Liverpool ta na da wa'adin zuwa ranar Juma'a da karfe 12 na rana agogon GMT ta daukaka kara a kan hukuncin.

Amma kuma idan kungiyar ba ta sami nasara ba za ta kasance ba tare da dan wasan ba har zuwa karshen watan Satumba.