Van Persie ya yi wa Arsenal kancal

Arsenal da manchester United
Image caption Manchester United ta jefa Arsenal cikin halin kaka-ni-kayi na zuwa gasar Zakarun Turai

Manchester United ta yi wa Arsenal kafar ungulu a kokarin 'yan gunners din na samun matsayin zuwa gasar Zakarun Turai ta gaba.

Arsenal wadda ke wasa a gida tana matukar bukatar nasara a wasan nata da Manchester United amma suka yi kunnen doki 1-1.

A yanzu Arsenal ce ta 4 a teburin Premier da maki 64 a wasanni 35.

Tottenham tana bi mata baya da maki 62 amma kuma wasanni 34.

Theo Wallcott ne minti biyu da shiga fili ya jefa kwallo ragar Man United a sanadin kuskuren Robin van Persie.

Sai dai kuma Van Persien ya rama kwallon ana gab da tafiya hutun rabin lokaci da fanareti.

Bacary Sagna ne ya kayar da Van Persien abin da ya sa alkalin wasa ya bada bugun daga kai sai mai tsaron gidan.

Kwallon ita ce ta 29 da dan wasan ya ci wa Manchester United a bana.

Ita ma manchester United ta rasa damar kammala gasar ta Premier da maki 95.