Reading da QPR sun fadi daga Premier

reading and qpr relegated
Image caption Reading da QPR sun yi mutuwar kasko a Premier

Reading da Queens Park Rangers sun fadi daga Premier bayan sun yi canjaras ba ci tsakaninsu.

Daman kungiyoyin biyu su ne na karshe a cikin kungiyoyi 20 a gasar ta Premier.

Sakamakon rashin wadda ta yi galaba a kan daya dukkanin kungiyoyin biyu ko da sun yi nasara a sauran wasanninsu uku za su sami maki 34 ne kawai kowacce.

A kakar wasanni mai zuwa za su yi wasa ke nan a gasar kasa da Premier ta Championship.

Reading ta koma Championship din ne bayan kakar wasanni daya a Premier.

Ita kuwa QPR za ta yi wasa a gasar ta kasa da Premier din ce a karon farko tun kakar wasanni ta 2010-11.