Aston Villa ta hau tudun mun tsira

Aston Villa thrashed Sunderland
Image caption Aston Villa ta tarad da Sunderland a Premier

Aston Villa ta lallasa Sunderland 6 -1 ta tsira da maki biyar daga hadarin faduwa daga gasar Premier.

Da nasarar yanzu ta zama ta 16 a Premier kuma ta na da maki 37 daidai da Sunderland wadda ke matsayi na 15.

Ron Vlaar ne ya fara ciwa Aston Villa kwallonta a minti na 31 minti daya da dakikoki 49 tsakani sai Danny Rose ya ramawa Sunderland.

A minti na 38 kuma sa Andreas Weimann ya sake jefa kwallo ta biyu a ragar Sunderland.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci sai Benteke ya rika jefa kwallaye ragar 'yan Sunderland din daya bayan daya har guda uku.

Farko a minti na 55 sannan minti hudu tsakani ya sake jefawa sai kuma a minti na 72 ya cike ta ukunsa kuma ta biyar din kungiyar tasa.

Saura mintuna biyu loakcin wasan na minti 90 ya cika sai Gabriel Agbonlahor ya cike ta shida a ragar Sunderland din.

Rashin nasarar ya jefa Sunderland cikin fafutukar neman tsira a Premier tare da makwabciyarta ta arewa maso gabashin Landan Newcastle ta 17 a Premier da maki 37 ita ma.

Nasarar ta Aston villa ta kuma jefa Wigan tsaka mai wuya saboda yanzu tana maki 5 tsakaninta da Aston Villa.