Real Madrid ta gudu ba ta tsira ba

Borussia Dortmund da Real Madrid
Image caption Real Madrid ta kasa zuwa wasan karshe na Zakarun Turai karo na uku

Borussia Dortmund ta fitar da Real Madrid daga gasar Zakarun Turai duk da nasarar da Real ta yi a kanta da ci 2-0.

A karawar da suka yi a gidan Real Madrid ta biyu a wasan kusa da karshe Benzema ya ci kwallon farko a minti na 82.

Minti shida tsakani kuma sai Ramos ya kara ta biyu, sai dai Real Madrid tana bukatar cin kwallaye uku ne ba ko daya ta yi galaba a kan Dortmund.

Saboda a wasan farko Dortmund ta ci su 4-1 a Jamus yanzu sakamakon ya kasance kungiyar ta Jamus tana da kwallaye 4 ta Spaniyan tana da 3.

Yanzu Borussia Dortmund za ta jira wadda zata yi nasara tsakanin Bayern Munich da Barcelona a wasansu ranar Laraba ta san wadda zata hadu da ita a wasan karshe.

A ranar 25 ga watan Mayu ne za a yi wasan karshe a filin wasa na Wembley ta Ingila