Za a yi gasar kwallon kafa a Darfur

Nicholas Musonye Babban Sakataren Cecafa
Image caption Nicholas Musonye ya ce wasu daga cikin filayen wasannin da kayayyakin gasar sun yi kyau sosai

Majalisar hukumomin kwallon kafa na gabashi da tsakiyar Afrika (Cecafa) ta ce yankin Darfur na yammacin Sudan da ke fama da rikici zai karbi bakuncin gasar kwallon kafarta ta kungiyoyi.

Kungiyoyin kwallon kafar da suka dauki gasar lig ta kasashensu a yankin su su ke shiga gasar.

Kungiyoyi 12 ne daga kasashen za su shiga gasar wadda da a ke saran farawa bayan 15 ga watan Yuni.

Majalisar ta ce kungiyar St. Eloi Lupopo ta Jamhuriyar Dumokradiyyar Congo na daga wadanda za su shiga gasar wadda za a yi a watan Yuni.

Babban sakataren majalisar kwallon kafar Nicholas Musonye ya shedawa BBC cewa kawo yanzu wata kungiyar Eriteria ba ta ba su tabbacin za ta halarci gasar ba.

Musonye wanda ya je yankin na Darfur domin duba filaye da sauran kayayyakin wasannin da za a yi amfani da su ya ce an kammala kashi 90 cikin 100 na shirin amma na rukunai biyu daga cikin uku.

Babban Sakataren ya ce an dauke gasar daga babban birnin Habasha ne Addis Ababa aka maida Sudan saboda Ethiopian ba za ta iya daukar nauyin gasar ba.

Kungiyar Young Africans ta Tanzania ce ke rike da kofin wanda ta dauka a 2012.