Butler na fuskantar zargin baiwa dawakai kwayoyi

Gerard Butler
Image caption Gerard Butler ya ce ya baiwa dawakansa magunguna amma ance masa ba haramtattu ba ne

Hukumar tseren dawaki ta Birtaniya ta na binciken wani mai horadda dawakan tsere kan zargin baiwa wasu dawakai magungunan da aka haramta.

Gerard Butler shi ne mutum na biyu da ya ke fuskantar irin wannan zargi.

Ya bayyana cewa ya yi wa da yawa daga cikin dawakan maganin raunukan da suka ji a gabobinsu.

Sai dai ya ce an tabbatar masa cewa magungunan da ya yi amfani da su ba haramtattu ba ne.

Hirar da Butler ya yi da jaridar Independent ta sa Hukumar tseren dawakin Birtaniya ziyarar bargar dawakinsa inda ta gano ana amfani da magunguna da dama da aka haramta amfani da su.

A ranar Alhamis aka haramtawa Mahmood Al Zarooni mai horadda dawakan tseren Godolphin shiga harkar tseren dawaki tsawon shekaru 8 saboda baiwa dawakai magungunan kara kuzari.