Sunderland ta kalubalanci korar Sessegnon

stephane sessegnon
Image caption Sunderland na fargabar rasa Sessegnon a wasanninta na gaba

Kungiyar Sunderland ta daukaka kara akan korar dan wasanta Stephane Sessegnon da alkalin wasa ya yi a lokacin karawarsu da Aston Villa.

Alkalin wasa ya baiwa dan wasan mai shekaru 28 katin kora saboda ketar da ya yi waYacouba Sylla a wasan nasu na ranar Litinin da Aston Villa ta ci su 6-1.

Kociyan kungiyar ta Sunderland Paolo Di Canio ya ce ''ba wani laifi ba ne mai tsanani ya iya kasancewa wani tarko ga alkalin wasa saboda daga nesa za ka ga kawar mugunta ce amma abin ba haka yake ba.''

Hukuncin korar tasa ya sa ba zai buga sauran wasannin da kungiyar wadda ke neman tsira daga Premier za ta yi a gida da Stoke da Southampton da kuma da Tottenham a waje ba.

A ranar Larabar nan wani kwamiti mai zaman kansa zai duba batun hukuncin da aka yi wa dan wasan dan Jamhuriyar Benin.

Sessegnon ya ci wa Sunderland kwallaye 7 a wasanni 39 a bana.

Kungiyar ta na da maki 5 sama da matakin faduwa daga Premier sai dai ta yi wasa daya fiye da Wigan ta 18 a tebur.