Chelsea ta kai wasan karshe

Chelsea V FC Basel
Image caption Chelsea ta kama hanyar daukan kofin Turai na biyu a kaka biyu a jere bayan ta yi waje da FC Basel

Kungiyar Chelsea ta kai wasan karshe na kofin Europa bayan da ta fitar da FC Basel da ci 5-2 a karawa biyu.

A karawar da suka yi ta biyu a gidan Chelsea Stamford Bridge Chelsean ta jefa musu kwallo 3-1, bayan a wasan farko daman ta ci su 2-1.

Mohamed Salah ne ya fara daga ragar Chelsea ana dai dai da tafiya hutun rabin lokaci.

Bayan an dawo ne da minti 5 Fernando Torres ya rama kwallon sannan minti biyu tsakani kuma Moses ya kara ta biyu.

Minti bakwai da cigaba da wasan ne sai David Luiz ya ci wa Chelsea kwallo ta uku. Da wannan nasara Chelsea ta kama hanyar daukar kofunan Turai biyu a shekaru biyu.

A ranar 15 ga watan Mayu Chelsean za ta yi wasan karshe a Amsterdam da Benfica wadda ta fitar da Fenerbahce da ci 3-2 gida da waje. A haduwarsu ta farko Fenerbahce ta ci Benfica 1-0 amma kuma a karawa ta biyu a gidan Benfica ita kuma ta rama da ci 3-1.