Ban yanke shawarar barin Madrid ba - Mourinho

Jose Mourinho
Image caption Jose Mourinho ya nuna aniyarsa ta barin Real Madrid

Jose Mourinho ya nace cewa har yanzu bai yanke shawara ko zai bar kulob din Real Madrid ba a karshen kakar wasanni ta bana.

Kocin na wannan magana ce duk da rohotannin da ke nuna cewa ya cimma yarjejeniya domin komawa kulob din Chelsea.

Chelsea dai ta ki cewa uffan game da rahotannin da ke cewa kocin dan kasar Portugal zai tabbatar da komawarsa kulob din a ranar 1 ga watan Yuli.

"Idan na cimma matsaya kan makomata, to iyali na ne za su fara sani, sai kuma shugaba da daraktan kulob din," a cewar kocin mai shekaru 50 da haihuwa.

"Ban yanke shawarar tafiya. Idan na tafi, to ba zan yi karin bayani ba."

Mourinho, wanda a baya ya nuna aniyarsa ta komawa gasar Premier ta Ingila ya kara da cewa: "Ina aiki ne da kwarewa kuma har yanzu ina da girmamawa da jin dadin aiki a wannan kulob din kamar yadda na yi a wata daya ko biyu da suka gabata.

"Za mu yi magana a kan makomata a karshen kakar bana."

Karin bayani