Chelsea ta casa Manchester United

Manchester United lost to Chelsea
Image caption Chelsea ta kara cigaba a fatanta na samun gurbin gasar Zakarun Turai

Chelsea ta bi Manchester United har gida ta lika mata daya mai ban haushi a gasar Premier.

A minti na 87 ne Juan Mata ya sheka kwallon da ta shafi Phil Jones a kafa ta fada ragar United.

Kafin cin alkalin wasa ya kori Rafeal na Manchester United bayan da ya bugi David Luiz a kafa cikin fushi.

Nasarar ta sa Chelsea ta zama ta uku daga ta biyar da maki 68 kuma tana da kwantan wasa daya da Tottenham.

Yanzu Manchester United wadda ta ci kofin na Premier tana da maki 85 a wasanni 36.

Manchester City na bi mata baya da maki 72 a wasanni 35, ita ma tana da kwantan wasa daya.