Wani dan kallo ya mutu a Scotland

Scotland
Image caption Lamarin ya haifar da rudani a filin wasa na Rugby Park

Wani mutum ya rasu a asibiti bayan da ya fadi a lokacin da ake tsakiyar wasan kwallon kafa a gasar Premier ta Scotland.

Mutumin da ke da shekaru 50 da doriya, ya samu bugun zuciya ne mintina biyar bayan dawowa daga hutun rabin lokaci a wasan Kilmarnock da Hibernian.

Masu bayar da agajin gaggawa sun kaiwa mutumin dauki har lokacin da motar asibiti ta isa filin wasan na Rugby Park inda aka wuce da shi asibiti.

Duka kociyoyin kulob din sun amince su dage wasan domin girmama dan kallon.

Filin wasan ya yi tsit a lokacin da jami'an lafiya suke duba mutumin a bangaren 'yan kallo.

Daga bisani kuma sai alkalin wasan ya dakatar da karawar a lokacin da ake 1-1. 'Yan wasa sun fice daga fili a lokacin da aka fahimci cewa lamarin ya kazanta.