Sunderland ta dan tsira da kunnen doki

Sunderland equalizes against Stoke
Image caption 'Yan Sunderland sun yunkuro a rabin lokaci na biyu kadan ya rage su yi galaba

Sunderrland ta yunkuro da 'yan wasa goma ta rama kwallon da Stoke City ta jefa mata ta samu muhimmin maki a kokarin da take na tsira a gasar Premier.

A farko-farkon wasan Jon Walters ya sa Stoke City a gaba ana minti tara da wasa inda ya daga ragar Sunderland.

Can kuma a kashin farkon na wasan alkalin wasa ya kori Craig Gardner na Sunderland bayan ya yi wa Adam na Stoke keta.

Sunderland ta samu kanta daga bakin a minti na 63 lokacin da John O'Shea ya rama kwallon.

Kwallon ita ce ta biyu da kyaftin din ya ci wa klub din a bana kuma ta baiwa Sunderland din damar zuwa matsayi na 15, maki uku tsakaninta da Wigan ta 18 a Premier wadda ta rage ko ta tsaira ko kuma ta fadi daga gasar.

Tuni daman Reading ta 19 da QPR ta 20 suka fadi daga gasar ta Premier.

A ranar Talatar nan Wigan za ta hadu da Swansea ta 9 a Premier mai maki 43