Masoya Dortmund 500,000 na son tikiti

Borussia Dortmund
Image caption Dortmund sun doke Real Madrid a wasan kusa da na karshe

Magoya bayan Borussia Dortmund dubu 500 ne suka nemi a sayar musu da tikitin kallon wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai.

Kulob din zai kara da takwarorinsu na Jamus Bayern Munich, a filin wasa na Wembley da ke Ingila a ranar 25 ga watan Mayu.

Sai dai an ware tikiti dubu 24 ne kawai saboda sayarwa magoya bayan Dortmund, domin kallon karon battan na karshe a gasar.

Masoya kulob din sun mika kimanin bukatar tikiti dubu 250, a cikin sa'oi 24, bayan karawar da kulob din ya yi a zagaye na kusa da na karshe a ranar Talatar da ta gabata.

A waje daya kuma mai tsaron gidan Dortmund, Roman Weidenfeller ya rattaba hannu a kan kwantiragin karin wa'adin zamansa a kulob din zuwa shekarar 2016.

Karin bayani