Za a yi wa Gerrad tiyata a kafada

 steven gerrard
Image caption A kwanakin nan ciwon kafadar da Gerrard ya ke fama da shi ya matsa masa

Za a yi wa kyaftin din Liverpool dan wasan Ingila Steven Gerrard aiki a asibiti saboda ciwon da yake fama da shi a kafadarsa a makon nan.

Dan wasan na tsakiya mai shekaru 32 ya buga dukkanin wasanni 36 da kungiyarsa ta yi a Premier daga farko.

A makonnin nan raunin nasa ya yi tsanani saboda haka klub din ya bukaci a yi masa tiyatar a nan kusa.

Dan wasan ba zai samu damar buga sauran wasannin klub din biyu da suka rage ba, da Fulham da kuma Queens Park Rangers.

Amma kuma ana saran zai warke har ya yi wasannin shirin shiga kakar wasanni ta gaba.

Saboda aikin da za ayi masa ba zai samu damar buga wasannin sada zumunta da Ingila za ta yi da Jamhuriyar Ireland ranar 20 ga watan Mayu.

Da kuma wanda za ta yi da Brazil ranar 2 ga watan Yuni.

Gerrard ya buga wasan da Liverpool ta yi canjaras ba ci da abiyar hamayyarta Everton ranar Lahadi.

Sakamakon da ya sa klub din ya tsaya a matsayi na 7 da maki 55 ya kasa wuce matsayin da ya zarta na 6 a gasar Premier.