David Moyes zai maye gurbin Sir Alex

David Moyes
Image caption Moyes ya fara wasa a Celtic ya gama a Preston inda suka yi wasa da Beckan yana matashi

kociyan Everton David Moyes ne zai gaji Sir Alex Ferguson wanda ya sanar da shirinsa na ritaya daga mukamin horar da 'yan wasan Manchester United.

A yau Alhamis ne ake saran bada sanarwar nadin Moyes mai shekaru 50 wanda shi ma dan yankin Scotland ne kamar Sir Alex.

Kociyan wanda yake tare da Everton tun 2002 ya gana da shugana klub din Bill Kenwright da yammacin jiya Laraba akan sabon aikin da ya samu.

Sai dai kuma zata iya kasancewa shi ne zai jagoranci kungiyar ta Everton a wasan da za ta yi da West Ham ranar Lahadi. Wasan shi ne zai kasance na karshe da zai jagoranci klub din a gida.