Darajar hannun jarin Man United ta fadi

Sir Alex Ferguson
Image caption Man U ta ce ba lalle ba ne wanda ya gaji Sir Alex ya yi nasara kamarsa

Darajar hannun jarin Manchester United ta fadi a kasuwar New York saboda fargabar abin da ka iya biyo bayan saukar Sir Alex daga mukamin kociyan kungiyar.

Labarin ritayar tasa ya bayyana ne bayan rufe kasuwannin hannayen jari na Amurka.

Da aka bude kasuwannin darajar hannun jarin kungiyar ta fadi da kashi hudu da rabi cikin dari.

Yanzu dai ana ta rade radin wanda zai gaji Sir Alex wanda ya ciyo kofuna 38 a tsawon shekaru 26 da ya yi a kungiyar.

Inda ake ambaton sunayen kociyan Everton David Moyes da kuma na Real Madrid Jose Mourinho.

Duk wanda ya samu mukamin zai gaji klub din da ke da dimbin bashi na fam miliyan 370 kuma wanda attajiran iyalin nan na Glazer ke iko da shi matuka.

Iyalan sun sayi klub din a kan kudi fam miliyan 790 a 2005 a wani ciniki da ke cike da takaddama da ya jefa shi cikin bashi.

Tun lokacin da iyalan na Glazers suka saka kungiyar cikin kasuwar hannayen jari ta new York a watan Agusta na 2012 darajarsa ta tashi da kashi 34 cikin 100.

Kuma sun sayar da miliyan 16 da dubu 700, kashi 10 cikin dari na hannun jarin.