Najeriya ta sauya shawara kan gasar Afrika

Nigerian Footballer
Image caption Sau biyu Najeriya na yunkurin zuwa gasar ta Afrika ba tare da nasara ba

Najeriya ta sauya shawara a kan kin shiga wasannin neman zuwa gasar Kofin Afrika ta 'yan wasan cikin gida ta 2014.

A watan Afrilu Hukumar kwallon kafa ta kasar ta ce ta janye daga wasannin neman shiga gasar saboda rashin kudi.

Yanzu Najeriyar zata yi wasa da Ivory Coast gida da waje a Calabar a watan Yuni domin neman gurbi a gasar da za a yi a shekara mai zuwa a Afrika ta kudu.

Sau biyu a baya 'yan wasan Najeriya Zakarun Afrika ba sa samun cancantar zuwa gasar.