Dawowar Mourinho alheri ne: Lampard

Lampard da Mourinho
Image caption Mourinho shi ne kociyan da ya fi kowa a duniya inji Lampard

Frank Lampard ya ce zai zama babban abin alheri idan Jose Mourinho ya dawo Chelsea.

Dan wasan na tsakiya mai shekaru 34 ya dauki kofunan Premier biyu da wasu manyan kofunan uku a tsawon shekaru uku da Mourinho yayi a klub din.

Masu lura da al'amura na ganin Mourinho wanda yanzu yake Real Madrid shi yafi dacewa ya maye gurbin kociyan kungiyar na yanzu Rafeal Benitez.

Lampard ya ce ya sha jin rade radi a baya amma kuma sai yaga wani kociya na dabam ya bayyana.

To amma a wannan karon bai san abin da zai kasance ba amma kuma ba shakka Mourinho yana daya daga cikin masu horar da 'yan wasa da suka fi idan ma ba a ace shi ne na daya a duniya ba.

Ko da aka tambayi Lampard wanda kwantiraginsa zai kare a karshen kakan nan ko idan Mourinho ya dawo Chelsea zai tsaya. Sai ya ce ''ba shakka amma dai a bari aga abin da zai kasance.

Ya ce ''ai daman a ko da yaushe ina cewa ina son in kare wasana a Chelsea.''

A karshen kakar wasannin nan kociyan rikon kwarya na Chelsea Rafeal Benitez zai gama aikinsa kuma ana ganin Mourinho ne wanda ya jagoranci klub din daga 2004 zuwa 2007 zai dawo ya maye gurbinsa.