Tottenham ta jirkito Arsenal kasa

Tottenham da Stoke
Image caption A haduwar Tottenham da Stoke sau biyar sakamakon yana kasance wa 2-1 ne

Fatan Tottenham na zuwa Gasar Kofin Zakarun Turai ya kara tabbata bayan da kungiyar ta yi nasara a kan Stoke City da ci 2-1.

Yanzu Tottenham wadda ta yi nasarar a gidan Stoke ta kawar da Arsenal daga matsayi na hudu a Premier yayin da 'yan Gunners din suka dawo na biyar.

Steven Nzonzi ne ya fara jefa kwallo ragar bakin minti uku kacal da fara wasan.

Bayan minti goma sha bakwai sai Clint Dempsey ya rama wa Tottenham, sannan kuma can an kusa tashi daga wasan a minti na 83 Emmanuel Adebayor ya ci ta biyu.

Sai dai kuma har yanzu Arsenal na da damar komawa matsayin ta hudu saboda wasanni biyu suka rage mata.

Inda za ta kara da Wigan da kuma Newcastle yayin da Tottenham wasa daya ya rage mata a gida da Sunderland .

Tottenham ta dogara ne ga rashin nasarar Arsenal a sauran wasannin biyu da suka rage ta samu damar dorewa a matsayin ta hudun kuma ta je Gasar Zakarun Turai.