Peter Odemwingie zai bar West Bromwich

Peter Odenwingie zai bar West Brom
Image caption Peter Odemwingie bayan kungiyarsa ta West Brom ba ya jituwa da kociyan Najeriya ma

Dan wasan Najeriya Peter Odemwingie na gab da barin West Bromwich, wadda suke takun saka da ita tun bayan da ya yi kokarin barin ta.

Mai horad da 'yan wasan kungiyar Steve Clarke ya ce a kakar wasanni ta gaba za su tantance matsayin dan wasan a klub din.

Ya kara da cewa ba ya jin dan wasan zai kasance a klub din a kakar wasanni ta gaba.

A 'yan watannin da suka gabata Odemwingie mai shekaru 31 ya yi ta samun kansa cikin takadda sakamakon kalaman da ya rika yi ta shafin intanet na twitter.

Kuma a watan Janairu ya yi yunkurin ficewa daga kungiyar ta West Brom ya koma Queens Park Rangers ba tare da izini ba abin da ya ci tura kuma tun daga sannan ba a sa shi sosai a wasa.