Pellegrini ya musanta komawa Man City

Manuel Pellegrini da Roberto Mancini
Image caption Mancini ya ce bai san dalilin Man City na kin karyata labarin daukar Pellegrini ba

Kociyan Malaga Manuel Pellegrini ya musanta rahotannin da aka bayar cewa zai maye gurbin Roberto Mancini a Manchester City.

A wata sanarwa da ya baiwa shafin Intanet na kungiyar Malaga Pellegrini ya ce ''ba wata tantama na musanta cewa ni ne sabon kociyan Manchester City.''

Ya kara da cewa ''ina da yarjejeniya da Malaga kan kada na tattauna da kowa kuma babu wata yarjejeniya da aka cimma da kowa.''

A watan Afrilu ne dai jami'an Manchester City suka gana da wakilin Pellegrini, Jesus Martinez wanda kuma shi ne ke wakiltar dan wasan tsakiya na Malaga Isco wanda aka ce Chelsea na nema.

Mancini ya ce bai san dalilin wannan ganawa ba A watan Nuwamba na 2010 Pellegrini ya koma Malaga bayan ya yi aiki da Real Madrid da kuma Villarreal.

A shekararsa ta farko a kungiyar ya jagoranci Malaga ta kammala gasar La Liga a matsayi na hudu ya kuma kai ta Gasar Zakarun Turai a karon farko.

Kungiyar ta kai wasan gab da na kusa da karshe na gasar Zakarun Turaikafin Dortmund ta fitar da ita, kuma yanzu ita ce ta shida a La Liga.

Malaga ba za ta shiga gasar kofunan Turai ba mai zuwa saboda basukan da bata biya ba.