PSG ta yi watsi da bukatar Real Madrid

Carlo Ancelotti
Image caption Real Madrid na neman Ancellotti da Chelsea ta kora Mourinho na son komawa Chelsea

Paris St-Germain ta yi watsi da bukatar Real Madrid ta neman mai horad da 'yan wasanta Carlo Ancelotti.

Shugaban kungiyar ta PSG Nasser al Khelaifi ya ce '' Real sun zo mun tattauna da su , na gaya musu yana da kwantiragi na sauran shekara daya.

A wurina zai ci gaba da zama a nan har badi.''

Sai dai kuma da aka tambayi Carlo Ancelotti game da batun sai ya ce, ''ba zan ce zan tafi ko zan tsaya ba sabo da ban tattauna da shugaban klub din ba ya zuwa yanzu.''

ancelloti wanda Chelsea ta kora a watan Mayu na 2009 bayan kammala kakar wasanni ba tare da daukar wani kofi ba ya jogaranci PSG ta dauki kofin Lig din Faransa a karon farko tun 1994.

Haka kuma Zlatan Ibrahimovic dan Sweden ya yi alkawarin ci gaba da zama a PSG.

Bayan da ya dauki kofin lig dinsa na takwas da kungiyar wadda ita ce ta shida da ya cimma wannan nasara da ita.

Dan wasan mai shekaru 31 ya dauki kofunan lig da Ajax da Inter Milan da Barcelona da AC Milan yanzu kuma da PSG.

Sauran kofunan lig biyu da ya dauka da Juventus an karbe su saboda samun kungiyar da laifin shirya magudin sakamakon wasa.