Hukumar hana shan kwayoyi ta matsawa Kenya

'Yan tseren kasar Kenya
Image caption Zargin shan kwayoyin kara kuzari ya mamaye harkar wasan tsere a Kenya

Hukumar yaki da ta'ammali da kwayoyin kara kuzari a wasanni ta duniya ta ce dole ne hukumomin Kenya su binciki zargin da ake yi wa 'yan tseren dogon zango na kasar na amfani da kwayoyi.

Ana zargin likitoci da masu hada magunguna da dama a kasar da laifin bai wa 'yan gudu kwayoyin kara kuzari.

A farkon shekaran nan aka dakatar da wasu 'yan wasan tsere uku da aka samu da laifin amfani da kwayoyin kara kuzari bayan an gwada su an gano hakan.

Sai dai shugaban hukumar guje-guje da tsalle-tsalle na Kenyan Isaiah Kiplagat ya dora alhakin rashin bin umarnin hukumar hana amfani da kwayoyin kara kuzarin ta duniya na kafa kwamiti mai zaman kansa don gudanar da bincike a kan ma'aikatar wasanni ta kasar.