Ba za a yi wa PSG bikin ba da kofi ba

Rikicin PSG
Image caption Akalla mutane 30 aka jikkata a lokacin arangamar ta magoya bayan PSG da 'yan sanda

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Faransa ta hana bikin mikawa kungiyar Paris St Germain kofin gasar Lig din kasar da ta dauka a bainar jama'a.

Hukumomi sun dauki matakin ne bayan rikicin da ya barke ranar Litinin da daddare yayin murnar nasarar cin kofin.

Da yake sanar da matakin hana bikin wanda ada za a yi ranar Larabar nan a zauren birnin Paris, Manuel Valls ya ce da alamu ba bu wani biki da za a yi na mika kofin a bainar jama'a a nan kusa.

Akalla mutane 30 aka raunata a lokacin da 'yan sanadan kwantar da tarzoma suka yi dauki ba dadi da masu tada zaune tsaye a dandalin Trocadero.