Arsenal ta fitar da Wigan daga Premier

Wigan ta fadi daga Premier
Image caption Arsenal ta kawo karshen Shekaru 8 na Wigan a Premier ta kuma koma gurbin Gasar Zakarun Turai

Wigan ta fadi daga gasar Premier bayan da Arsenal ta warwasa ta da ci 4-1, 'yan Gunners din suka kuma koma gurbin zuwa Gasar Zakarun Turai a Premier.

Lukas Podolski ne ya fara zura kwallo a ragar Zakarun Gasar Kofin Kalubale na Ingilan da kai cikin minti 11 na wasan, kafin Shaun Maloney ya rama gab da tafiya hutun rabin lokaci.

Sai dai kuma bayan an dawo kashi na biyu na wasan Theo Walcott ya sake daga ragar bakin a minti na 63, minti biyar tsakani kuma Podolski ya sake nasa ta uku.

Minti uku kuma daga nan sai Aaron Ramsey ya cike kwallo ta hudun da suka maida kungiyar inda ta fito, gasar Championship ta kasa da Premier shekaru takwas baya.

Yanzu Arsenal ce ta hudu a tebur da maki 70 inda ta kawar da Tottenham wadda ta dawo ta biyar da maki 69, yayin da ya rage wasa daya a kammala gasar.

Idan Arsenal ta yi nasara a wasanta da Newcastle ranar Lahadi za ta tabbata a matsayin da zai bata damar zuwa Gasar Zakarun Turai.

Yanzu Wigan ta bi layin Reading da Queens Park Rangers na fice wa daga Premier inda ta ke da maki 35 a wasanni 37, yayin da ya rage wasa daya a kammala gasar ta Premier ta bana.

Haka kuma Sunderland da Aston Villa hankalinsu ya kwanta daga hadarin faduwa daga Premier bayan da Wigan ta cike gurbi dayan da ya rage da rashin nasarar da ta yi.

Reading da Manchester City

A daya wasan da aka yi na Premier, Reading a gidanta ta sha kashi 2-0 a hannun Manchester City wadda ta kori kociyanta Roberto Mancini.

Nasarar wadda mataimakin Mancini Brian Kidd ya jagoranci kungiyar ita ce farko bayan barin kociyan dan Italiya.

Sergio Aguero ne ya fara cin kwallo ta daya minti 40 da wasa , can kuma a kashi na biyu na wasan ana saura minti 10 lokaci ya cika Edin Dzeko da ya shigo daga baya ya kara ta biyu.

Nasarar ta tabbatar wa Manchester City matsayinsu na biyu a Premier.