Kamaru ta yi watsi da sunayen 'yan wasa

kociyan kamaru jean-paul akono
Image caption Dangantaka na kara tsami tsakanin kociyan Kamaru Jean-Paul Akono da hukumar kwallon kasar

Hukumar kwallon kafa ta Kamaru ta yi watsi da sunayen 'yan wasan da kociyan kasar mai barin gado Jean-Paul Akono ya fitar na wasannin sada zumunta da neman zuwa gasar Kofin Duniya.

Hukumar ta ki amincewa da sunayen 'yan wasan da ya zaba na wasannin da kasar za ta yi a watan Yuni.

Hakan na nufin da alamu a sauya 'yan wasan da kociyan ya zaba.

Akono ya ce dai-dai ne a gare shi ya yi zaben ita kuwa hukumar ta ce ba'a bi ka'ida ba wajen zaben.

Da alamu yanayin na iya kara bata dangantakar kociyan na rikon kwarya da hukumar kwallon wadda ta sanar da neman mai maye gurbinsa ba tare da saninsa ba.

Kuma a lokacin da ake tattaunawa da shi domin maida shi na dun-dun-dun.

Ranar 2 ga watan Yuni Kamarun za ta yi wasan sada zumunta da Ukraine.

San nan ta yi wasan neman zuwa gasar Kofin Duniya ta rukuni na 9 (Group I) da Togo ranar 9 ga watan na Yuni da kuma Jamhuriyar Dumokradiyyar Congo ran 16 ga watan.

Bayan wasu 'yan wasa da kociyan ya sake basu damar dawowa kungiyar kasar ya kuma gayyato wasu guda 8 da suke wasa a cikin gida.